Bangaren kasa da kasa; Cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta jaddada wajabcin yaki da jahilci a cikin kasashen musulmi, bisa la'akari da matsalar karancin karatu a cikin wasu yankuna da ke cikin wasu kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar, babban sakatarenta Abdulaziz Al-tuwaijari ya bayyana cewa, cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta jaddada wajabcin samar da wasu shirye-shirye na yaki da jahilci a cikin kasashen musulmi, bisa la'akari da matsalar karancin karatu da ake samu a cikin wasu yankuna da ke cikin wasu kasashen.
Ya ci gaba da cewa dole gwamnatocin kasashen musulmi su mike tsaye wajen tabbatar da cewa matsalar jahilci a tsakanin al'ummominsu ta zama labari, domin kuwa samun kasashe musulmi a wannan zamani da mutane da ba su iya rubutu ko karatu ba babban ci baya ne.
649185