IQNA

Musulunci Na Da Matsayi A rayuwar Al'ummar Rasha

13:23 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990465
Bangaren kasa da kasa; Fitaccen marubucin nan dan kasar rasha Yury Mikhailov ya bayyana cewa, addinin Musulunci na da matsayi na musamman a cikin rayuwar zamantakewar al'ummar kasar.



Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na Muhit an bayyana cewa, Fitaccen marubucin nan dan kasar rasha Yury Mikhailov ya bayyana cewa, addinin Musulunci na da matsayi na musamman a cikin rayuwar zamantakewar al'ummar kasar Rasha, kamar yadda al'adun Musulunci suke da matsayi har wala yau a wurin mutanen kasar ta Rasha.

Ya ce babban dalilin hakan kuwa ba komai ba ne illa saboda addinin Musulunci addini ne da ya ginu kan adalci da kare hakkoki, da kiyayya da zalunci da danniya kan masu rauni, addini na taimako da tausayi.

650335



captcha