IQNA

An Girmama Mahardata Kur'ani 5 A Kasar Morocco

13:24 - September 08, 2010
Lambar Labari: 1990468
Bangaren kasa da kasa; An Girmama wasu mahardata kur'ani mai tsarki su biyar da suka halarci gasar Danja da ke kasar Morocco, wadanda suka taka gagarumar rawa a wannan gasa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na map cewa An Girmama wasu mahardata kur'ani mai tsarki su biyar da suka halarci gasar Danja da ke kasar Morocco, wadanda suka taka gagarumar rawa a wannan gasa.

A wajen taron da aka gudanar an girmama wadanda suka shiga cikin gasar kuma suka samu matsayi na daya da matsayi na biyu har zuwa na uku a dukkanin bangarori da aka gudanar da gasar.

Cibiyar kula da harkokin kur'ani ta birnin Danja ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan taro tare da halartar wasu daga cikin kungiyoyi gami da cibiyoyin addinin kasar.

650351



captcha