IQNA

Mai Zanen Batunci Ga Musulunci Ya Samu Kyauta

11:22 - September 09, 2010
Lambar Labari: 1990983
Bangaren kasa da kasa; Shahararren mutumin nan da ke yin zanen batunci ga addinin Musulunci musamamn ma ga manzon ya samu kyautar 'yancin bayyana ra'ayi a ranar laraba daga gwamnatin kasar Jamus.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani lbari da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran AFP an bayyana cewa, mutumin nan da ya shahara wajen yin zanen batunci ga addinin Musulunci musamamn ma ga manzon ya samu kyautar 'yancin bayyana ra'ayi a ranar laraba daga gwamnatin kasar Jamus.

Rahoton ya ci gaba da cewa mahkuntan Jamus sun bayyana shi a matsayin wani mutum wanda ke da kwazo bayyana ra'ayinsa da kuma kare manufofi na dimokradiyya, a akan haka ya cancanci girmamawa ta musamamn daga gwamnatin Jamus.

Daga cikin wadanda suka hallara wajen mika masa kyautar yabo ta batunci ga addinin Musulunci har babbar waziriyar kasar Jamus Angela Mikel, da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.

651223



captcha