Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarata cewa, a wani rahoto day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamrf an habarta cewa, an bude wani shafin syanar gizo na Musulunci na kasashe masu magana da harshe guda amatsayin harshen kasa, domin samun fahimtar koyarwar addinin muslunci ta bai daya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shafi an bude shi ne a cikin harshen rashanci, wanda zai amfanar da kasashe da dama da suke magana da wannan harshe a cikin Asia da ma gabacin nahiyar turai.
Daga cikin kasashen da za su yi amfani da wannan shafi har da kasar Rahsa, Azaibaijan, Ukraine, Georgia, Tajikistan, Kyrgystan Turkmenistan da dai sauransu.
652537