Bangaren kasa da kasa; Bayan da fetsararren kiristan na Amurka ya janye daga batun kone kur'ani da ya yi niyar yi a ranar 11 ga watan satumba, wani mutum mai gaba da addinai a kasar Australia ya kone kur'ani da kuma bible.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran France Press cewa, bayan da fetsararren kiristan na Amurka ya janye daga batun kone kur'ani da ya yi niyar yi a ranar 11 ga watan satumba, wani mutum mai gaba da addinai a kasar Australia ya kone kur'ani da kuma bible a kasar.
Rahoton ya ce mutumin ya yi hakan ne domin ya nuna wa duniya cewa babu ruwansa da kowane addini, duk kuwa da cewa shi kirista ne, wanda hakan ke nuni da irin tsananin gabar da ake nuna wa musulmi da Musulunci a cikin kasashen tirai.
A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin musulmi a kasar Austaralia Sheikh Muhammad Wahid ya yi kakkausar suka kan hakan, tare da bayyana cewa hakan zai jawo gagarumin fushin musulmi a duniya.
653582