IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Makon Al'adu A Kasar Canada

12:33 - September 18, 2010
Lambar Labari: 1995930
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da tarukan makon al'adu a kasar Canada wanda bangaren nazarin ilmomin zamantakewa na da ke birnin Saint-Gearges ya dauki nauyin shiryawa a cikin makon mai zuwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na editionbeace cewa, za a gudanar da tarukan makon al'adu a kasar Canada wanda bangaren nazarin ilmomin zamantakewa na da ke birnin Saint-Gearges ya dauki nauyin shiryawa a makon gobe.

Daliban da suke gudanar da nazari a wannan bangre ne suke daukar nauyin shrya wannan zaman taro, wanda za a gudanar a karo na 4, bayan gudanar da makamantansa a cikin shekaru uku da suka gabata.

Babbar manufar gudanar da zaman taron dai ita ce bayyana manufofin addinai da kuma kusanto da fahimtarsu, musamman ma manyan addinai kamar kiristanci, Musulunci yahudanci da kuma Hindus.

656637







captcha