IQNA

Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Kasar Libya

13:51 - September 18, 2010
Lambar Labari: 1996059
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka yi wa lakabi Alfatih a birnin Tripoli na kasar Libya, wadda cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arab online an habarta cewa, za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka yi wa lakabi Alfatih a birnin Tripoli na kasar Libya, wadda cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin mako mai zuwa.

Bayanin ya kara da cewa wannan gasa na daya daga cikin irinta da ake gudanarwa a kasar a kowace shekara, da ke samun halartar makaranta da mahartda daga sassa daban-daban na kasashen musulmi.

Gasar an kasa ta zuwa kashi uku, da bangaren hardar kur'ani baki daya, sai kuma bangaren hardar rabin kur'ani da kuma rubu'I, sai kuma bangaren karatu ma akan wannan tsari.

656842

captcha