IQNA

Mayar Da Martani Kan Kone Kur'ani Dole Ya Zama A Hankalce

12:08 - September 19, 2010
Lambar Labari: 1996786
Bangaren kasa da kasa; Mayar da martani kan kone kur'ani mai tsarki wasu masu tsananin gaba da addinin muslunci suka yi a kasar Amurka, dole ne mayar da martanin musulmi ya za a hankalce tare da dabi'a irin t addinin Musulunci.



A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da babban daraktan cibiyar harkokin kur'ani ta garin Nasiriyya a kasar Iraki Ra'ad Adnan Al-nasiri ya bayyana cewa, Mayar da martani kan kone kur'ani mai tsarki wasu masu tsananin gaba da addinin muslunci suka yi a kasar Amurka, dole ne mayar da martanin musulmi ya za a hankalce.

Ya wadanda suka yi hakan hakika mutane da mabiya addinin kirista ke kallonsu a matsayin marassa ladabi da dabi'a irin ta 'yan adamataka, balalnta koyarwar irin ta addinin kiristanci, a kan haka ba a kallonsu a matsayin masu addini a ko a cikin kiristancin.

Saboda haka ya zama wajibi kan musulmi su mayar da martani kansu amma cikin tsari da yin amfani hankali da kyawawan dabiu irin wadanda addinin Musulunci ya koyar da musulmi.

656892





captcha