Bangaren kasa da kasa; Makarantar koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki ta kasar Belgium da ke da babban ofishinta a birnin Brussel fadar mulkin kasar, ta fara daukar sabbin dalibai masu karatu a matakai daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato wani labari daga shafin sadarwa na escb na yanar gizo cewa, makarantar koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki ta kasar Belgium da ke da babban ofishinta a birnin Brussel fadar mulkin kasar, ta fara daukar sabbin dalibai masu karatu a matakai daban-daban na karatu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan makaranta tana daukar dalibai domin horar da su kan karatun kur'ani mai tsarki, amma a wannan karon tsarin daukar dalibai da kuma hanyoyi tafiyar da tsarin horar da su zai sha banban.
Yanzu haka dai an dauki dalibai da dama da za su samu horo a cikin wannan shekara, kamar yada tsarin zai ci gaba da tafiya a haka a nan gaba.
658129