IQNA

An Gudanar Da Zaman Taro Kan Cika Shekara Da Rushe Baki'a

14:10 - September 21, 2010
Lambar Labari: 1998631
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zaman taro kan cika shekara guda cur da rushe mabartar nan mai tarihi da matsayi na musamamn a cikin addinin Musulunci ta Baki da ke birnin Madina mai alfarma.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya samu daga kamfanin dillancin labaran kur'ani na nun an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro kan cika shekara guda cur da rushe mabartar nan mai tarihi da matsayi na musamamn a cikin addinin Musulunci ta Baki da ke birnin Madina mai alfarma wanda gwamnatin wahabiyan saudiyya ta rusa.

Rahoton ya ce an gudanar da wannan zaman taro ne a birnin Karbala mai alfarma da ke kasar Iraki, tare da halartar wasu daga cikin malaman addini gami da marubuta da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar.

Gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta dauki matakin rushe makabartar Baki ne domin bakantawa mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah, da suke ziyartar kabrukan iyalan gidan manzon Allah(SAW) da ke wurin.

658758




captcha