IQNA

Keta Alfarmar Kur'ani Mai Tsarki Tsararren Lamari Ne

15:07 - September 22, 2010
Lambar Labari: 1999545
Bangaren kas ada kasa; Keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka bayan da wani mai kiran kansa malamin addinin kirista ya yi kira da hakan, wani shiri da aka tsara tun kafin wannan lokaci.



A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da Nabi Maknun editan jaridar Adis Adams ta kasar Ethiopia ya bayyana cewa, keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka bayan da wani mai kiran kansa malamin addinin kirista ya yi kira da hakan, wani shiri da aka tsara tun kafin wannan lokaci da aka aiwatar da shi.

Nabi Maknun wanda ya tarjama littafan marigayi Imam Khomeini (RA) a cikin harshen Amharik harshen da ake amfani da shi a hukumance a kasar Ethiopia, ya bayyana aika-aikar ta tsirarun kiristocin Amurka da cewa tana daya daga cikin manyan munann ayyuka da aka taba aikatawa a bayan kasa.

Ya kira dukkanin musulmi da su kwana da sanin cewa wannan makirci ne na makiya Musulunci da addinin kiristanci, da nufin kawo gagarumar baraka tasakanin mabiya addinan biyu a duniya.

659554



captcha