IQNA

Taron Bayar Da Kariya Ga Kur'ani A Kasar Turkiya

15:08 - September 23, 2010
Lambar Labari: 1999935
Bangaren kasa da kasa; za a gudanar da wani zaman taro a kasar Turkiya mai take bayar da kariya ga kur'ani mai tsarki, da nufin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto labari daga shafin sadarwa na media 73 cewa, Za a gudanar da wani zaman taro a kasar Turkiya mai take bayar da kariya ga kur'ani mai tsarki, da nufin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka a cikin kasa da makonni biyu da suka gabata.

Kungiyar nan ta masoya manzon Allah ta kasar Turkiya ita ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan zaman taro, inda za a gabatar da jawabai daban-daban dangane da matsayin musulmi kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki.

Haka nan kuma taron zai yi dubi zuwa ga matsayin manzon Allah (SAW) da kuma kur'ani mai tsarki, da kuma yin kira da gurfanar da dukkanin wadanda suke da hannu wajen aikata wannan mummunan aiki.

660566



captcha