Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Turkiya Jihan cewa, 'Yan sandan kasar Birtaniya sun damke wasu wasu mutane shida da ake zarginsu da kone kur'ani mai tsarki a kasar, wanda aka buga labarinsa a shafin internet.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin mutanen ana zarginsu da hannu wajen kone kur'ani a ranar 11 gawatan satumba da wani malamin kirista mai gaba da Musulunci ya sanar, wanda kuma an saka abin da suka yi a cikin shafin yanar gizo.
Bayan watsa kone kur'ani da aka yi da aka saka a shafin yanar gizo a kasar Birtaniya, 'yan sanda sun shiga bincike kuma sun kame mutanen da suka yi hakan, inda musulmi suke neman da a hukunta su.
661526