IQNA

Mutanen Masar Masoya Ahlul-Bait (AS) Da Mabiyansu

15:46 - September 25, 2010
Lambar Labari: 2000968
Bangaren kasa da kasa, Ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar masar ya bayyana cewa al'ummar masar masoya iyalan gidan manzon Allah (SAW) ne da kuma mabiyansu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na iraqgreen.net cewa, ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Masar Mahmud Hamdi Zaqzuq ya bayyana cewa al'ummar masar masoya iyalan gidan manzon Allah (SAW) ne.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wata tawagar mutanen kasar Iraki da ta kai ziyara a kasar Masar, da nufin kara bunkasa dangantakar addinin a tsakanin dukkanin al'ummomin kasashen biyu masu dadden tarihi.

Ya jaddada cewa wajibi ne musulmi su hada kai tare da yin watsi da duk wani banbancin mazhabobi matukar dai suna son cimma manufofinsu na isar da sakon addinin Musulunci ga sauran al'ummomi.

661553

captcha