IQNA

Fira Ministan Malazia Ya Karfafa Malamai Wajen Yada Fikirar Addini

10:24 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002119
Bangaren kasa da kasa; Fira ministan kasar Malazia ya karfafa malaman addinin Musulunci wajen yada tunani da koyarwar wannan addini ga sauran al'ummomi na duniya, da nufin kara samar da fahimtar juna tsakanin addinai.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Bernama ya watsa ya bayyana cewa, tsohon fira ministan kasar Malazia ya karfafa malaman addinin Musulunci wajen yada tunani da koyarwar wannan addini ga sauran al'ummomi na duniya, da nufin kara samar da fahimtar juna tsakanin addinai na duniya.

Tsohon fira ministan na kasar Malazia Mahatir Mohammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro da aka shirya a birnin Botrajaya na kasar, inda jami'ar birnin ta ba shi digirin girmamawa.

Mahatir Muhammad dai na daya daga cikin fitattun shugabanni na kasashen musulmi da suke nuna adawa da tsarin danniya da babakere na kasashen yammacin turai a kan sauran al'ummomin duniya musamman ma musulmi.

662793






captcha