IQNA

An Buga Littafin Rayuwar Allamah Fadlollah A Tehran

10:23 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002125
Bangaraeen kasa da kasa; An buga tare da yada littafin rayuwar marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hossein Fadlollah babban malamin addini na kasar Labanan a birnin Tehran.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren kula da tace rubuce-rubuce na jamhuriyar Musulunci cewa, An buga tare da yada littafin rayuwar marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hossein Fadlollah babban malamin addini na kasar Labanan a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci.

Bayanin ya kara da cewa wannan littafin ya mayar da hankali kan muhimman abubuwan da malamin ya mayar da hankali kansu a lokacin rayuwarsa, da nufin ganin sun samu wurin zama a cikin al'ummar musulmi.

Daga cikin wadannan batutuwa kuwa hard a batun hadin kan musulmi, da kuma kusanto da fahimtar juna tsakanin dukkanin mazhabobin musulmi na duniya baki daya, tare da yi wa juna kyakyawan zato.

Allamah Fadlollah dai ya kasance daya daga cikin malaman da suka shahara a duniya shi'a wajen ganin an samu daidaiton fahimta da girmamam ra'ayoyin juna a tsakanin mazhabobin musulmi.

662856




captcha