IQNA

Wahabiyawa Sun Nemi A Hana Watsa Shirin Tashar Shi'a

10:23 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002127
Bangaren kasa da kasa, Wani lauya karkashin tasirin akidar wahabiyanci a kasar Masarn ya shigar da kara a gaban kotu da ke neman a hana watsa shirye-shiryen tashoshin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kan tauraron dan adam na nile sat.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Brana an bayyna cewa, wani lauya karkashin tasirin akidar wahabiyanci a kasar Masarn ya shigar da kara a gaban kotu da ke neman a hana watsa shirye-shiryen tashoshin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kan tauraron dan adam na nile sat daga kasar ta Masar.

Wannan lauya wanda aka tabbatar da cewa yana yi wa wahabiyawa aiki ne tukuru, ya shigar da karar ne bisa hujjar cewa tashoshi irin su Alanwar suna keta alfarmar akidun Ahlu sunna, akan haka yana neman kotun ta yanke hukunci haramta watsa shirye-shiryen ta kan tauraron dan adam na kasar.

Karar lauyan yan wahabiayawan ta zo ne a daidai lokacin dad a suke tsananta daukar matakai na a kasashen Saidiyya da Masar wajen hana mabiya mazhabar ahlul bait gudanar da harkokinsu daidai da yadda kundinntsarin mulkin kasashensu ya ba su dama.
662900



captcha