Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar Al-shaq Ausat an bayyana cewa, Wata majami'a ta bayar da makarantarta a ga daliban musulmi a yankin Blackbourn na kasar Birtaniya, da nufin kara kyautata dangantaka tsakanin mabiya addinan biyu.
Rahoton ya ci gaba da cewa makarantar wadda take karkashin majami'ar katolika, an bayar da ita ne ga wata cibiyar ilimi ta musulmi da ke kusa da ita, wadda take kara bunkasa tare da samun dalibai musulmi.
Majami'ar ta bayar da wannan wuri ne da nufin kara dankon zumunci tsakanin mabiya addinan biyu, wadanda suke zaune lafiya da juna a kasar ta Birtaniya.
663195