IQNA

Taro Mai Taken Musulunci Da Musulmi A Birnin Chicago

13:32 - September 28, 2010
Lambar Labari: 2003138
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Chicago na kasar Amurka mai taken musulmi da Musulunci da zai samu halartar jagoron musulmi na birnin da wasu yankuna da ke kusa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Arab News an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a birnin Chicago na kasar Amurka mai taken musulmi da Musulunci da zai samu halartar jagoron musulmi na birnin da wasu yankuna da ke kusa da birnin.

Bayanin ya ci gaba da cewa a zaman taron za a yi bahasi kan yanayin rayuwar musulmin kasar Amurka da kuma irin matsalolin da suke fuskanta na rayuwar zamantakewa tsakaninsu da sauran mutanen da musulmi ba.

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ita ce ta shirya gudanar da zaman taron, inda babban sakataren kungiyar Ihsan Auglo zai fara bude taron da bayaninsa, daga bisani kuma sauran masana da aka gayyata.

663986







captcha