IQNA

Jaddada Wajabcin Samar Da Abincin Halal Ga Musulmin Turai

16:23 - September 28, 2010
Lambar Labari: 2003330
Bangaren kasa da kasa; Daya daga cikin fitattun masana kan harkar abincin halal a kasar Belgium Bruno Bernard ya bayyana cewa, dole a samar wa musulmi da wadatattun kayayyakin abinci na halal.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kuna na kasar Kuwait an habarta cewa, daya daga cikin fitattun masana kan harkar abincin halal a kasar Belgium Bruno Bernard ya bayyana cewa, dole a samar wa musulmi da wadatattun kayayyakin abinci na halal a cikin kasar.

Masanin ya bayyana cewa musulmi suna da abubuwan da addininsu ya yarje musu da su ci, kuma bas u damar su samar da irin wadannan abubuwa daya ne daga cikin hakkokinsu da ya kamata a kare.

Yanzu haka dai wannan kira da masanin ya yi mahukuntan kasar ta Belgium suna yin nazari kansa, domin samun hanyar da za a warware wa musulmin wannan matsala.

663753



captcha