IQNA

ISESCO Ta Jaddada Muhimmancin Kare Muhalli A Musulunci

13:29 - September 29, 2010
Lambar Labari: 2003864
Bangaren kasa da kasa; Babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ya jaddada muhimmancin tsafta da kare muhalli a mahanga irin ta addinin Musulunci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasashen musulmi ISESCO Abdulaziz Usman Al-tuwaijari ya jaddada muhimmancin tsafta da kare muhalli a mahanga irin ta addinin Musulunci.

Sakataren kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Aman na kasar Jordan, wanda ya fara ayyukansa a jiya.

Ya ci gaba da cewa Musulunci yana da mahanga ta musamman akan tsafta a cikin rayuwar dan adam, inda hakan ya hada da batun tsafta ta muhalli, ta jiki da dai sauransu.

Taron yana samun halartar masana da malamai gami da jami'ai daga kasashen musulmi da na larabawa, da kuma wasu kasashen Asia.

664679













captcha