IQNA

Aikin Kafofin Yada Labaran Larabawa Ne Su Tona Asirin Isra'ila

13:29 - September 29, 2010
Lambar Labari: 2003872
Bangaren siyasa da zamantakewa, Ministan sadarwa na kasar Syria ya bayyana cewa babban sakon da ya kamata kafofin yada labaran kasashen larabawa su isar ga sauran al'ummomin duniya, shi ne tona asirin haramtacciyar kasar Isra'ila.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran sana na kasar Syria ya bayyana cewa, ministan sadarwa na kasar Syria ya bayyana cewa babban sakon da ya kamata kafofin yada labaran kasashen larabawa su isar ga sauran al'ummomin duniya, shi ne tona asirin haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya.

Ministan harkokin sadarwar na kasar Muhsin Balal ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro kan sadarwa akasashen larabawa da aka gudanar jiya abirnin Damascus fadar mulkin kasar.

Inda ya jaddada wajabcin zage dantse a tsakanin kafofin yada labaran larabawa domin bayyana wa duniya hakinin abin da yake faruwa na zaluncin Isra'ila.

664821



captcha