IQNA

Hezbollah Da Jabhatul Amal Sun Jaddada Wajabcin Hadin Kai A Labanan

13:30 - September 29, 2010
Lambar Labari: 2003877
Bangaren siyasa da zamantakewa, Kungiyar Hizbullah da kuma Jabhatul amal islami sun jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin al'ummomin kasar Lababan, domin fuskantar makircin makiya baki daya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga reshensa na yada labarai a Labanan an bayyana cewa, kungiyar Hizbullah da kuma Jabhatul amal islami sun jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin al'ummomin kasar Lababan, domin fuskantar makircin makiya.

Dukkanin bangarorin biyu sun jaddada hakan ne a cikin wani bayani na bai daya da suka fitar, da nufin fadkar mutanen kasar kan fitinar mazhaba da addini da ake neman haifarwa a cikin kasar a cikin 'yan lokutan nan.

Daga karshe dukkanin bangarorin biyu sun kafa wani kwamiti na bai daya, wanda zai kula da tunbar juna da kuma hada bayanai na baui daya da suka iya fitarwa a nan gaba.

664772


captcha