Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sama ya yi nuni da cewa Wani sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a cikin yankunan Palastinawa ya ya yi da cewa shugaban kwarya-kwaryan cin gishin kan palastinu Mahmud Abbas ba zai iya kare mutuncin mutanensa ba.
An gudanar da wannan jin ra'ayin jama'ar ne a cikin yankunan palastinawa, inda kimanin kashi 72 cikin dari digo daya daga cikin plastinawan da aka ji era'ayinsu suka nuna cewa Mahmud Abbas ba zai iya kare mutuncinsu a tattaunawar da yake da yahudawa ba.
Mafi yawan al'ummar palastinu dai sun yi imanin cewa tatatunawar da bangaren mahmud Abbas ke gudanarwa tare da yahudawa ba zata taba haifar musu da mai ido ba.
665352