Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfain dillancin labaran turiyegaz cewa wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari kan wani masallaci a garin Selweard a kasar Holland da nufin ci gaba da takura wa musulmin kasar da kuma nuna kyama ga musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa jim kadan bayan bazuwar labarin jami'an tsaron kasar Holland sun isa wurin, amma sun bayyana cewa mutanen sun bar wurin kuma ba yi barna akan ginin masallacin ba, sai sun yi rubuce-rubucen batunci ga addinin muslunci.
Kasar Holland na daya daga cikin kasashen turai da musulmi suke fuskantar matsaloli da dama, da suka hada tsangwama da kuma takura musu, baya ga kalaman batunci da suke ji kullum rana ta Allah.
665363