Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa ya bayyana cewa duk wata tataunawar sulhu tsakanin palastinawa da yahudawa karakshin ci gaba da gina matsugunnai ba ta da ma'ana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labara wafa an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa ya bayyana cewa duk wata tataunawar sulhu tsakanin palastinawa da yahudawa karakshin ci gaba da gina matsugunnai bata lokaci ne kawai.
Ya ci gaba da cewa tattaunawa kai tsaye tsakanin bangarorin palastinawa da yahudawa na nufin samun hanyar kawo karshen rikicin da bangarorin biyu suke yi tun tsawon shekaru, sakamakon mamaye yankunan palastinawan da yahudawa suka yi.
Amr Musa ya ce idan har yahudawan ba su dakatar da gina matsugunnan da suke yi a cikin yankunan palastinawa ba, mene ne ma'anar ci gaba da wannan tattaunawa.
665562