IQNA

Za A Gudanar Da Baje Kolin kayan Halan A Glasco

12:15 - September 30, 2010
Lambar Labari: 2004457
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro na abincin halal a birnin Glasco na kasar Birtaniya, wanda shi ne karo na farko da za a gudanar da shi a kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran prlog cewa za a gudanar da wani zaman taro na abincin halal a birnin Glasco na kasar Birtaniya, wanda shi ne karo na farko da za a gudanar da shi a kasar ta Birtaniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje kolin kayyakin halal wanda shi ne na farko a kasar Birataniya zai kunshi kayyaki da ake sana'antawa daga kasashen msulmi, da kuma wasu kayan da ake yi a turai amma da ba su yi hannun riga da hukuncin Musulunci ba.

Kamfanoni da dama daga kasashen musulmi sun nuna sha'awar kai kayansu a wannan baje koli, da nufin kara yawan kayan halal a kasashen turai.

665559



captcha