IQNA

Tarukan Shahadar Imam Sadiq (AS) A Birnin Viena

16:03 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2006018
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da tarukan shahadar Imam Sadiq (AS) a birnin Viena fadar mulkin kasar Switzerland, a babbar cibiyar muslunci ta Imam Ali (AS) da ke cikin birnin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da samu ta yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan shahadar Imam Sadiq (AS) a birnin Viena fadar mulkin kasar Switzerland, a babbar cibiyar muslunci ta Imam Ali (AS) da ke cikin birnin na Viena.

Wannan zaman taro zai gudana ne a daren yau Asabar, da kimanin karfe 7 na daren yau agogon Viena, inda za a gabatar da jawabai dangane da rayuwar Imam Sadoq (AS) tare da halartar masana da malaman musulmi da suke birnin.

Imam Ja'far Sadiq (AS) shi ne limamin iyalan gidan manzon Allah (SAW) na shida, kuma ya yi shahada ne a hannun sarakunan Abbasiyawa da suka zalunci iyalan gidan, ya yada ilimin addinin muslunci da duniya ke amfana da shi.

666947





captcha