Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO cewa, an bayar da wata lambar yabo ga baban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta musulmi ISESCO Abdulaziz Usman Al-tuwaijari a Ireland.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan Babban malamin musulmi a kasar Ireland shi ne aya mika wannan kyauta ta musamman ga Al-tuwaijari, wanda ya bayyana ta da cewa kyauta ce ta zaman lafiya da fahimtar juna.
Tuwaijari ya karbi kyautar ne alokacin da yake halartar wani zaman taro da aka shirya a birnin Doblin fadar mulkin Ireland da nufin yin bahasi kan yawaitar kyamar muslunci da musulmi a nahiyar turai.
666944