Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar yaum sabi ta kasar Masar cewa, an fitar da wani littafi na mu'ujizar kur'ani a tarihance a cikin mujalladi biyu a cikin harshen larabci, wanda marubucin nan dan kasar Masar Zaglul Alnajjar ya rubuta kuma aka fitar da shi a cikin wannan mako.
Wannan littafin ya yi tsokaci kan wasu daga cikin kissoshin kur'ani mai tsarki da tarihi ya tabbatar da su, da kuma yadda kur'ani mai tsarki ya bayar da masaniya kan abubuwa da dama da ba a sani ba a cikin tarihi.
Kur'ani mai tsarki ya ambaci kissosi da suka zo a cikin littafai masu tsarki da aka safkarwa wasu annabawa, kamar su attaura da injila da sauransu, wadanda su kansu kur'ani ya ambace su da kuma abin da ba su ambata ba.
668258