Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na turkiyegazeesi an habarta cewa, cibiyar kasuwancin nan ta birnin London za ta yi gwanjon wasu kayayyakin tarihin muslunci a cikin birnin London da suka hada da kayayyakin India da dai sauransu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gwanjo za a gudanar da shi a babban ginin cibiyar da ke tsakiyar birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, inda za kawo yayyaki na tarhi daban-daban da suka kai kimanin dari hudu.
Kayan sun hada da wasu abubuwa da aka samu a lokacin mulkin sarakunan Usmaniyya a cikin nahiyar turai, gami da wasu kayayyaki da aka samu daga kasar India da suke nuna tarihin muslunci.
668660