IQNA

An Nuna Fitattun Shafukan Muslunci A Baje Kolin Sadarwa Na Digital

12:46 - October 09, 2010
Lambar Labari: 2009011
Bangaren kasa da kasa, An nuna wasu shafukan muslunci na yanar gizo da suka shahara a duniyar musulmi a baje kolin kayayyakin sadarwa na digital da ake gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na baje kolin kayan sadarwar muslunci an bayyana cewa, an nuna wasu shafukan muslunci na yanar gizo da suka shahara a duniyar musulmi a baje kolin kayayyakin sadarwa na digital da ake gudanarwa a birnin Tehran.

Shugaban bangaren gudanarwa na baje kolin Mahdi Salim ya bayyana cewa, gudanar da irin wannan baje koli na da matukar amfani ga masu sha'awar ayyuka na sadarwa, domin kuwa za su samu masaniya kan kayan aiki.

Yanzu haka dai an baje kolin kayan sadarwa da suka da na'uroti na daukar hoto mai motsi da maras motsi, da kuma kayan daukar rahotanni da watsa su, gami da kayayyaki dangin na'ura mai kwakwalwa.

670594






captcha