Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabic people an bayyana cewa, A wani jawabi da ya gabatar a gaban taron kungiyar hadin kan kasashen muslmi ta OIC da ake gudanarwa a birnin Istanbul na kasar Turkiya, shugaban kasar Abdullah Gol ya bayyana cewa wajibi ne duniyar musulmi ta yi aiki tukuru domin warware matsaloli da dama da suka addabi mabiya addinin muslunci.
Ya ci gaba da cewa al'ummar musulmi na fuskantar matsaloli da dama, da suka hada da karancin abinci a wasu yankuna, na kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi, wanda a cewarsa ya kamata a warware irin wadannan matsaloli.
Ya kara da cewa daga cikin irin wadannan matsalolin da muslmi suke fuskanta har da rashin hadin kai, wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da suke raunata musulmi a dukkanin bangarori.
670580