IQNA

Cibiyar Musulunci Ta London Ta Yi Na'am Da Bayanan Sheikhul Azhar

14:39 - October 10, 2010
Lambar Labari: 2010015
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar muslunci ta birnin London karkashin shugabancin wakilin jagora ta yi na'am da bayanan shekhul Azhar dangane da fatawar jagoran juyin juya halin muslunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Cibiyar muslunci ta birnin London karkashin shugabancin wakilin jagora ta yi na'am da bayanan shekhul Azhar dangane da fatawar jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran.

A cikin wata wasika da wakilin jagora ya aike wa bababn malamin jami'ar Azhar ya bayyana cewa; mun yi na'am da wannan mataki da ka dauka wanda ko shakka babu zai taka gagarumar wajen hada kan musulmi.

Wakilin ya jagora ya ce ko shakka babu matakin da shugaban Azhar din ya dauka na gamsuwa da wannan fatawa zai bayar da wata dama ta hada kan bangarorin musulmi bayan fitar da wannan fatawa.

670977



captcha