Bangaren kasa da kasa, An buga tare da fitar da littafin nan mai bayani kan matsayin dangantaka tsakanin Musulunci da Vatican, wanda wani marubuci dan kasar Jamus ya rubuta kuma aka tarjama zuwa wasu yaruka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran Kuna na kasar Kuwait an habarta cewa, an buga tare da fitar da littafin nan mai bayani kan matsayin dangantaka tsakanin Musulunci da Vatican, wanda wani marubuci dan kasar Jamus ya rubuta kuma aka tarjama zuwa wasu yaruka na duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa marubucin wannan littafi ya yi kokarin bayyana dangantaka tsakanmin addinin muslunci da kiristanci a matsayin dangataka da addinai biyu da aka safkar daga sama da suke da kusanci da juna.
An tarjama wannan littafi zuwa wasu yaruka daga ciki kuwa hard a harshen larabci, inda aka kaddamar da wanda aka tarjama zuwa larabci a kasar Oman tare da halartar masana.
673454