Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na marcojournal cewa, gwamnatin kasar Morocco ta bukaci da a dauki matakan da suka dace domin karshen kyamar musulmi a cikin yankunan nahiyar turai da kewaye.
Ridwan bil arabi wanda shi ne bababn sakataren cibiyar yada al'adu ta gwamnatin Morocco ya bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya a dauki karan tsana a dorawa musulmi a cikin nahiyar turai.
Ya ce ya zama wajibi kan gwamnatocin kasashen musulmi da na turai su dauki dukkanin matakan kawo karshen wanna dabi'a maras adalci ga musulmi.
674268