IQNA

Za A Gudanar Da Wani Shiri Na Koyar Ilimin Tajwidi A Kutaif

9:20 - October 16, 2010
Lambar Labari: 2013066
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri na horar da daliban makarantu ilmin sanin ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki a makarantun yankin Kutaif da ke gabacin kasar Saudiyya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid an bayyana cewa, za a gudanar da wani shiri na horar da daliban makarantu ilmin sanin ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki a makarantun yankin Kutaif da ke gabacin kasar Saudiyya da ke mabiya mazhabar iyalan gidan manzo.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri na daya cikin shirye-shiryen da cibiyoyin addini musamamn ma na kur'ani suka mayar da hankali kan aiwatar da shi, musaman ma bayan kammala karatukan lokutan hutun bazaar.

Yankin Kutaif na mabiya mazhabar shi'a a gabacin kasar Saudiya na da cikin yankunan da ake mayar da hankali da koyar da 'yan makaranta karatun kur'ani mai tsarki da ilmin tajwidi.

675417




captcha