IQNA

Limamin Najaf Ya Yi Na'am Da Jawabin Ahmadinejad Kan Isra'ila

11:33 - October 17, 2010
Lambar Labari: 2014160
Bangaren kasa da kasa, Limamin birnin Najaf Ashraf Sayyid Sadruddini Kubanchi ya nuna farin cikinsa dangane da ziyarar da shugaban kasar Iran ya kai kasar Lebanon, da kuma furucin da ya yi na neman haramtacciyar kasar Isra'ia da ta mika wuya, kuma yahudawan sahyniya su koma inda suka fito.


Kamfanin dilancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na kubanchi an bayyana cewa, limamin birnin Najaf Ashraf Sayyid Sadruddini Kubanchi ya nuna farin cikinsa dangane da ziyarar da shugaban kasar Iran ya kai kasar Lebanon, da kuma furucin da ya yi na neman haramtacciyar kasar Isra'ia da ta mika wuya, kuma yahudawan sahyniya su koma kasashensu na asali.

Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar juma'a a masallacin Hubbarn Imam Amirul mumin Ali (AS) a ranar juma'ar da ta gabata.

Kubanci ya bayyana cewa yahudawan sahyuniya da suka zo palastinu basu da wani dalili na mayar da kasar larabawa a matsayin kasarsu, tare kashe mabuta kasar.

675778



captcha