Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya samu daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasa an bayyana cewa, a bugu na dari da talatin da shida na mujallar harkokin addini da siyasa ta Alwahda an yi nazari kan yadda wasu auka keta alfarmar alkur'ani mai tsarki a cikin kasar Amurka.
Wannan bugu ya mayar da hankali kan dalilan da suka sanya irin wadannan mutane daukar wannan mataki a halin yanzu bayan da suka yi ta daukar wasu matakan cin zarafin muslmi a wasu kasashen ba tare da an kula su ba.
Nazarin ya tabbatar da cewa keta alfarmar kur'ani na tattare da wata boyayyar manufa ta yahudawan sahyuniya da nufin kawo wani gagarumin rikici tsakanin musulmi da kirista a duniya.
678275