Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan harda da karatun kur'ani mai tsarki a garin Nasiriyya na kasar Iraki, wanda zai kwashe tsawon watanni biyu ana gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar harkokin kur'ani mai tsarki ta kasar Iraki an bayyana cewa an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan harda da karatun kur'ani mai tsarki a garin Nasiriyya na kasar Iraki, wanda zai kwashe tsawon watanni biyu ana gudanarwa a birnin.
Rahoton ya ce shirin ya samu karbuwa daga makaranta da mahardata na birnin na Nasiriyya, yayin da wasu daga cikin cibiyoyin kur'ani na wasu laduna a kasar suka nuna shawa'arsu ta shiga cikin shirin.
Bayan kammala wannan shiri na bayar da horon ga makaranta da mahardata za a bayar da takardun shedar kammala samun wannan horo da cibiyar ayyukan kur'ani ta dauki nauyin aiwatarwa.
678275