Bangaren kasa da kasa, Mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Turkiya sun fara gudanar da shirye-shiryen tarbar watan muharram, wanda a cikinsa ne a ke gudanar da tarukan tunwa da shahadar Imam Hussain (AS) a ranar Ashura.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na zainabiyya cewa, mbiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Turkiya sun fara gudanar da shirye-shiryen tarbar watan muharram, wanda a cikinsa ne a ke gudanar da tarukan tunwa da shahadar Imam Hussain (AS) a ranar Ashura a birnin Karbala.
Bayanin ya ci gaba da cewa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Turkiya suna gudanar da taruka na juyayin shahadar Imam Hussain (AS) tare da iyalan gidan manzon a ranar Ashura.
A wannan shekrar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar turkiya suna shirin gudanar da wani gagarumin taro a ranar Ashura, wanda za a gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar.
681899