Bangaren kasa da kasa:Giret Waldarz dan majalisa a kasar Holand mai tsotsoran ra'ayi da bakar nuna gaba ga addinin Musulunci marubucin littafin fitina a wata tattaunawa da mujallar kasar Jamus Ashpigol ya sake cin mutuncin Musulunci da yin bakaken kalamai kan addinin musuluncin kan haka a wata mai zuwa zai sake gurfana a gaban kulliya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci tai ran bayan ta nakalto daga majiyar hurriyet ya watsa rahoton cewa; Giret Waldarz dan majalisa a kasar Holand mai tsotsoran ra'ayi da bakar nuna gaba ga addinin Musulunci marubucin littafin fitina a wata tattaunawa da mujallar kasar Jamus Ashpigol ya sake cin mutuncin Musulunci da yin bakaken kalamai kan addinin musuluncin kan haka a wata mai zuwa zai sake gurfana a gaban kulliya. Wannan dan majalisar mai tsautsauran ra'ayi da bakar gaba ga addinin Musulunci a wannan karo ma ya sake tabbatar da bakar adawa da kiyayya da yake yi wa addinin Musulunci da musulmi a fadin kasar ta Holand da ma duk inda suke a duniya kuma wannan yana nuni da yadda yake son haddasa fitina da rikici na addini a duniya.
694356