Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar kamfanin dillancin labarai na AFP na kasar Faransa ya watsa rahoton cewa'; wasu mutane da ba san ko suwane ne ba sun aike da wata wasika zuwa ga masallacin Istraburg na Faransa da a cikin suke yin barazanar fitar da su daga cikin wannan kasa.Wannan babban barazana ce da ke nuni karara da yadda musulmi a kasar ta Faransa ke fuskantar tsanani da nuna masu karan tsana da kyama sabanin sauran mabiya addinai na duniya.
695340