IQNA

Malaman Shi'ar Kasar Bahrain Sun Nuna Adawarsu Da Ziyarar Yahudawa A Kasar

15:38 - November 16, 2010
Lambar Labari: 2033382
Bangaren kasa da kasa; komitin malaman shi'a a kasar Bahrain sun fitar da wata sanarwa da a cikinta suke nuna adawarsu da duk wani mataki na barin tawagar yahudawan sahayoniya su ziyarci wannan kasa kuma wannan tawaga nada dangantaka ta kud da kud da sahayoniyawan Amerika.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Aba'a ya watsa rahoton cewa; komitin malaman shi'a a kasar Bahrain sun fitar da wata sanarwa da a cikinta suke nuna adawarsu da duk wani mataki na barin tawagar yahudawan sahayoniya su ziyarci wannan kasa kuma wannan tawaga nada dangantaka ta kud da kud da sahayoniyawan Amerika.Ali Raham mukaddashin shugaban komitin malaman shi'a a Bahrain ya bayyana cewa; labarin nan bad a jimawa ba wata tawagar yahudawan Sahayoniya na kusa da Yahudawan Sahayoniya masu tsautsaran ra'ayi na Amerika za su ziyarci kasar Bahrain lamarin da ke nuni da halin ko in kula na dubban shahidan kasar da wadanda suka samu raunuka da rasa muhallansu karkashin zaluncin yahudawan Sahayoniya.

696116

captcha