IQNA

Komitin Musulmin Faransa Sun Yi Allah Wadai Da Cin Fuska Ga Masallaci A Kasar

13:12 - November 29, 2010
Lambar Labari: 2039564
Bangaren kasa da kasa; komitin musulmi a kasar Faransa CFCM a a jiya ne ya fitar da wata sanarwa da a cikin wannan bayani ya ke yin Allah wadai da yadda ake cin fuska da kaita hurumin masallati a garin Marmand .




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya nakalto daga majiyar labarai ta gwamantin Faransa AFP ya watsa rahoton cewa; komitin musulmi a kasar Faransa CFCM a a jiya ne ya fitar da wata sanarwa da a cikin wannan bayani ya ke yin Allah wadai da yadda ake cin fuska da kaita hurumin masallati a garin Marmand .Takurawa da cin fuska kan musulmi da kuma guraren ibadarsu ba wani sabon abu ban e ba a faransa kuma irin dokokin da gwamnatin Faransa ke zartarwa da magangani na batanci a jawaban mahukumtan wannan kasar day an siyasa tun kafi da bayan hawan Sarkozy kan mulkin kasar ya kara rura wutar wannan matsala.

703109

captcha