IQNA

Za A Watsa Shirye-Shiryen Ashura A Talabijin Din Turkiya

10:31 - December 02, 2010
Lambar Labari: 2040938
Bangaren kasa da kasa, Za watsa shirye-shirye da tarukan ashura a cikin watan muharram kai tsaye a gidan talabijin din kasar Turkiya TRT tare da bayar da bayar da dama ga malamai su gabatar da jawabai.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na masallacin zainabiyya cewa, Za watsa shirye-shirye da tarukan ashura a cikin watan muharram kai tsaye a gidan talabijin din kasar Turkiya TRT tare da bayar da bayar da dama ga malamai su gabatar da jawabai da ake gudanar a wurin tarukan.

Bayanin ya ci gaba da cewa mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Turkiya ne za su shirya gudanar da tarukan na ashura kamar yadda suka saba gudanarwa a cikin kowane watan muharram, duk da irin canje-canjen da ka samu a cikin wannan shekara.

Gidan talabijin din TRT ya fara watsa shirye-shiryen ashura tun daga cikin shekara ta 2007, musamman tarukan da ake gudanarwa na wannan munasaba mai albarka a babban masallacin nan na Zainabiyya da ke cikin birnin Istanbul fadar mulkin kasar.

704601








captcha