Kamfann dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar al-raya ta kasar Qatar an bayyana cewa, kayayyakin rubutun kur'ani mai tsarki da mu'assar darul Rashid ta kasar Syria ta baje a baje kolin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Doha na kasar Qatar ya samu karbuwa da ga masu halartar taron baje kolin.
Rahoton ya kara da cewa wannan mu'assa ta gabatar da wasu muhimman abubuwa da suka kebance ta, da suka hada da kayayyakin rubutu da kuma wasu abubuwa da ta rubuta tare da daukar nauyin buga su da suka danganci kur'ani mai tsarki, da hada da kanann littafai masu dauke da byanan ayoyi da dai sauransu.
Bayan haka kuma cibiyar ta fadada ayyukanta ta bangaren samar da hanyoyin yada ilmomin kur'ani ta hanyar yanar gizo da kuma na'ura mai kwakwalwa, inda ta samar da sabbin fayafan karatun kur'ani mai tsarki da aka nada a cikin fayafani daban-daban.
Daga cikin kuwa har da wadanda suke dauke da karatun kur'ani daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, inda akan saka tilawar kur'ani mai tsarki daga makaranta kamar goma a cikin faifai daya.
704535