Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada wakilansa da wani makarancin kur'ani dan kasar Algeria Abdulkarim Hamdush ya bayyana cewa, yin koyi da fitattun makaranta kur'ani mai tsarki da suka shahara a duniyar musulmi kamar su Abdulbasit ido rufe a tashin farko bai dace da mai koyon karatun kur'ani da bai san ma'anoninsa ba, domin hakan zai kawar da shi daga abin da ya kamata ya fara sani.
A cikin zantawar makarancin ya bayyana cewa ba aibi ba ne yin koyi da fitattun makaranta kur'ani na duniya, amma hakan ya fi dacewa ga makarancin da ya san kur'ani sosai, kuma ya san ilmomi na kaidojin karatun kur'ani da banbancin kira'oi gami da ma'anar abin da yake karantawa.
Ya kara da cewa fitattun makaranta kur'ani kur'ani mai tsarki da suka shahara a duniya da kuma ake alfahari da su, sun riga sun nisa cikin sanin hanyoyi na karatun kur'ani, inda sukan karanta shi da kir'ai daban-daban ba tare da sun gwama wata kira'a da wata ba.
704659