Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Kuwait a zagaye na biyu, tare da halartar manyan jami'an ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na jaridar Al-rayi ta kasar Kuwait cewa, za a gudanar da gasar harder kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Kuwait a zagaye na biyu, tare da halartar manyan jami'an ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar ta kuwait.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar harder kur'ani na daya daga wadanda ake gudanarwa akowace shekara a kasar a matsayi na kasa da kasa, inda take samun halartar wakilan cibiyoyin kur'ani daga sassa daban-daban na duniya, musamman ma daga kasashen musulmi.
Babban jami'ai mai kula hulda da jama'a na ma'aikatar kula da harkokin addini a Kuwait ya bayyana cewa kimanin kasashe 50 za su samu halartar wannan babbar gasar harder kur'ani mai tsarki da za a gudanar a kasar.
Ya kara da cewa bayan kamala wannan gasa, za a bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka nuna kwazo wajen gasar, daga cikin kyuatukan kuwa hard a kudu da kum allunan bangirma.
705596